Isa ga babban shafi

Tedros ya zargi kasashen duniya da nuna wa bakake wariya

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya zargi kasashen duniya kan yadda suke nuna banbanci dangane da rayukan bakaken fata da farare wajen gudanar da ayyukan jinkai lura da abin da ke faruwa a kasar Ukraine.

Tedros Adhanom Ghebreyesus
Tedros Adhanom Ghebreyesus REUTERS - POOL New
Talla

Gebreyesus ya ce irin yadda kasashen suka mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan jinkai a Ukraine ya saba da yadda ake gudanar da su a wasu sassan duniya musamman idan matsalar ta shafi bakaken fata.

Shugaban Hukumar ya ce yana da kyau irin yadda ake kaiwa Ukraine dauki saboda yadda rikicin kasar ke yi wa kasashen duniya illa, amma kuma matakin ya ribanya yadda ake yiwa Yankin Tigray da Yemen da Afghanistan da Syria da kuma wasu yankunan duniya.

Gebreyesus ya ce ya zama wajibi ya bayyana gaskiyar abinda ke faruwa akan yadda duniya bata dauki mutane a matsayin abu guda ba, kuma fadin hakan na kona masa zuciya saboda yadda yake ganin lamarin.

Shugaban Hukumar wanda ya fito daga Yankin Tigray wadda ke fama da tashin hankali yace tun bayan tsagaita wutar da akayi, Majalisar Dinkin Duniya tace za’a dinga kai akalla motoci 100 na kayan agaji kowacce rana, amma ya zuwa motoci 20 kacal suka kai kayan daga 2,000 da ya dace ace sun je yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.