Isa ga babban shafi

Birtaniya za ta tarkata bakin-haure zuwa Rwanda

Birtaniya za ta tura bakin-haure da sauran masu neman mafaka da suka tsallako mashigin ruwan kasar zuwa can Rwanda, karkashin wata yarjejeniya mai sarkakiya da kasashen biyu suka cimma.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson AFP - MATT DUNHAM
Talla

Gwamnatin Birtaniya ta dauki matakin ne da zummar rage adadin bakin-hauren da ke daukar kasadar shiga cikin kasar .

A yayin gabatar da jawabinsa a kusa da Dover da ke yankin kudu maso gabashin Ingila, Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya bayyana cewa, daga yau, duk wanda ke shigowa cikin Birtaniya ta barauniyar hanya da kuma wadanda suka shiga cikin kasar ba bisa ka’ida ba tun daga ranar 1 ga watan Janairu, to babu shakka za a tarkata su a mayar da su can kasar Rwanda.

Johnson ya ce, Rwanda na da wadatar tsugunar da dubban mutane a cikin shekaru masu zuwa.

Duk da cewa Rwanda na take hakkin bil’adama, amma Firaministan ya bayyana ta a matsayin daya daga cikin kasashen duniya mafiya kwanciyar hankali, inda ta yi shura saboda karbar bakin-haure a cewarsa.

Dama ‘yan Birtaniya sun zabi Mista Johnson ne biyo bayan alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zabe cewa, zai rage kwararar bakin haure masu shiga kasar ta barauniyar hanya, amma sai dai matsalar ta ma ci gaba da tsananta ne bayan darewarsa kan karaga.

Sama da mutane dubu 28 ne suka isa Birtaniya bayan sun tsallaka mashigin ruwan kasar daga Faransa a cikin kananan kwale-kwale a shekarar bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.