Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci Rasha ta mika wuya ga kotun ICC

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ya bukaci Rasha da ta bai wa kotun duniya ta ICC hadin-kai wajen gudanar da bincike game da yiwuwar aikta laifukan yaki a Ukraine.

Antonio Guterres kewaye da sojoji a Ukraine
Antonio Guterres kewaye da sojoji a Ukraine REUTERS - GLEB GARANICH
Talla

A yayin wata ziyara da ya kai garin Bucha da ke wajen babban birnin Kyiv, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar ya ce, yana goyon bayan kotun ICC, yana mai kira ga Rasha da ita ma ta amince ta bai wa kotun hadin kai domin gudanar da bincike kan laifukan yaki a Ukraine.

Guterres ya ce, idan ana maganar laifukan yaki, to babu ma abin da ya fi yakin kansa girma wajen laifi.

Garin na Bucha inda Guterres ke ziyara, nan ne a aka gano gawarwakin daruruwan fararen hula bayan sojojin Rasha sun janye daga garin.

A karon farko kenan da babban magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya ke ziyara a Ukraine tun bayan da Rasha ta fara kaddamar da farmaki kan kasar, yayin da ya kewaye garuruwa da dama a cikin kasar ta Ukraine.

Guterres ya bayyana wannan yakin a matsayin rashin hankali da ya auku a karni na 21, yana mai cewa, yaki bala’i ne.

A bangare guda, masu shigar da kara na gwamnatin Ukraine sun ce a yau Alhamis, sun fara bincikar wasu sojojin Rasha 10 da ake zargi da aikata laifukan yaki a Bucha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.