Isa ga babban shafi
Amurka - Ukraine

Amurka na shirin karin tallafin dala biliyan $33 ga Ukraine

Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da katafaren shirin tallafi, da ya kunshi dala biliyan 33, don taimakawa Ukraine da makamai domin yakar Rasha da ta mamaye ta, inda ya yi gargadin cewa, mika wuya ga Rashan ba zabi bane ga kasashen yammacin Turai da Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden yayin wani jawabi a fadar White House, 21/04/22.
Shugaban Amurka Joe Biden yayin wani jawabi a fadar White House, 21/04/22. AP - Evan Vucci
Talla

Yayin da ya ke jawabi a fadar White House, shugaban na Amurka ya kuma gabatar da kudurin wasu sabbin dokoki da za su bayar da damar amfani da kadarorin attajiran Rasha da aka kwace a karkashin takunkuman da aka kakaba musu, wajen biyan diyya ga ‘yan Ukraine sakamakon barnar da sojojin kasar ta Rasha suka yi musu, tun bayan yakin da suka kaddamar a karshen watan Fabarairu.

Biden ya kuma bayyana cewa tabbas Amurka na kashe makudan kudade wajen mara wa Ukraine baya a yakin da take yi da Rasha, sai dai ya ce babu wani zabi da ya wuce cigaba da yin gwagwarmayar dakile manufar shugaban Rasha Vladimir Putin, domin gaza yin hakan zai janyo hasarar kudaden da suka zarce na yanzu.

Dangane da zargin da jami'an Rasha da kafofin yada labaran kasar suka yi cewa sojojinsu na gwabza yaki ne da kasashen yammacin Turai baki daya, a maimakon kasar Ukraine kadai, Biden cewa yayi har yanzu basu taba kai hari kan Rasha ba, Amurka na taimaka wa Ukraine ta kare kanta ne daga mamayar Rasha.

Akan matakin da katafaren kamfanin iskar gas na Rasha Gazprom ya dauka na katse gas din ga kasashen kungiyar tsaro ta NATO da kasashen EU Bulgaria da Poland kuwa, Biden ya ce Amurka ba za ta bar Rasha ta kuntatawa kasashen ba bisa ka’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.