An yi bikin ranar ma'aikata ta duniya
Ranar Lahadi aka yi bikin ranar ma’aikata ta duniya, wanda aka saba gudanarwa a duk ranar 1 ga watan Mayu a kasashe daban daban.
Wallafawa ranar:
Dubun dubatar masu zanga-zanga a sassan duniya sun mamaye tituna don bikin wannan rana, tare da matsa lamba ga hukumomi wajen ganin sun inganta ‘yancin ma’aikata.
Hotunan da ke yawo a kafafen yanar gizo sun nuna yadda dubban mutane suka yi gangami a kasar Sri Lanka, da Turkiyya, da India da Pakistan, har ma da Girka, da Faransa da dai sauran kasashe da dama.
Jama'a da kungiyoyin kwadago a biranen nahiyar Turai sun fito kan tituna domin gudanar da jerin gwano tare da sakonnin bukatu ga gwamnatocinsu, musamman a kasar Faransa inda aka yi amfani da hutun na karrama ma'aikata a matsayin lokacin gangamin nuna adawa da sabon shugaban kasar Emmanuel Macron da ya sake lashe zabe.
A Turkiya, ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun kame masu zanga-zangar da dama da suke kokarin isa dandalin Taksim na Istanbul don gudanar da gangamin nuna adawa da matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kaya ya haifar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu