Isa ga babban shafi

Gurbacewar muhalli ya haifar da mutuwar mutane miliyan 9 a duniya - Bincike

Wani binciken masana ya bayyana cewar gurbata muhalli yayi sanadiyar hallaka mutane miliyan 9 a duniya a shekarar 2019, abinda ke nuna karuwar matsalar dake da nasaba da sarkewar numfashi.

Matasa na murnar samun ruwan sama a wani yanki Jamhuriyar Nijar
Matasa na murnar samun ruwan sama a wani yanki Jamhuriyar Nijar © Rousslan Dion, Bonne Pioche Cinéma - 2021
Talla

Binciken da gudanar yace illar da gurbata muhalli ke haifarwa ya zarce wadanda yaki da ayyukan ta’addanci da zazzabin cizon sauro da cutar HIV da tarin fuka da amfani da miyagun kwayoyi tare da shan giya ke haifarwa.

Wata yarinya Damana dake kauyen Tatiste a Jamhuriyar Nijar lokacin da take alwala
Wata yarinya Damana dake kauyen Tatiste a Jamhuriyar Nijar lokacin da take alwala © Rousslan Dion, Bonne Pioche Cinéma - 2021

Sakamakon binciken yace gurbata iska da ruwa da kuma kasar da Bil Adama ke yi baya kashe mutane kai tsaye, amma kuma ya kan haifar da cututtuka irin su bugun zuciya da sankara da sarkewar numfashi da amai da gudawa tare da wasu cututtuka daban daban.

Binciken ya bayyana gurbata muhalli a matsayin babbar barazana ga lafiyar Bil Adama wanda ke iya zama illa ga rayuwar al’umma baki daya.

Sakamakon binciken ya bayyana cewar gurbacewar iska a matsayin abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane miliyan 6 da dubu 700 a shekarar 2019 a fadin duniya saboda matsalar da ake samu wajen amfani da man fetur da sabbin dabarun samun makamashi.

Jagoran binciken Richard Fuller na Cibiyar kula da lafiya da kuma yaki da gurbata muhalli ta ‘Global Alliance on Health’ ya kuma ce gurbata muhalli da sinadarai masu guba na yiwa tsire tsire illa.

Sakamakon binciken yace kusan kowanne mutum guda dake mutuwa daga cikin mutane 6 a duniya na da nasaba da cutar da ta biyo bayan gurbacewar muhalli daga binciken da akayi a shekarar 2015, abinda ke bada adadin mutane miliyan 9 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.