Isa ga babban shafi

Duniya ba za ta amince da kisan da Rasha ta yi ba - Faransa

Faransa ta ce kisan da Rasha ta yi wa jama’ar yankin Bucha abu ne da duniya ba za ta kara amincewa da shi ba, kuma dole ne a dakatar da faruwar irinsa ko ina a duniya har abada.

Wasu daga cikin 'yan uwan mutanen da aka kashe a Bucha
Wasu daga cikin 'yan uwan mutanen da aka kashe a Bucha AP - Emilio Morenatti
Talla

Sabuwar Ministar Harkokin Wajen Faransan Catherine Colonna ce ta bayyana hakan, inda ta ce yunkurin kisan kare-dangin da Rasha ta yiwa al’ummar yankin Bucha abin kunya ne kuma tsantsar rashin imani ne.

A bayanin na Uwargida Catherine lokacin da ta ziyarci kasar Ukraine, a matsayin nuna goyon bayanta a yakin da take yi da Rasha, ta ce kisan ba abu ne da duniya ba za ta kara lamunta ba.

A cewarta, Faransa na bai wa wadanda harin Rasha ya ritsa da su cikakken goyon baya, kuma Faransa zat a yi duk mai yiwuwa don tabbatar da zaman lafiya a Ukraine.

Daruruwan ‘yan Ukraine ne suka rasa rayukansu a yayin harin da Rasha ta kai Bucha, sai dai kuma tuni sojojin Rasha suka musanta harin da ake alakantawa da aikata laifukan yaki.

Colonna ta kuma yi fatan za a dauki matakin shari’a kan Rasha tare da gaggauta tattara duk wasu hujjoji da za su tabbatar da laifinta a gaban shari’a, a cewarta hakan ne kadai zai saukaka wa iyalan wadanda aka kashe radadin rashin ‘yan uwansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.