Isa ga babban shafi

Ukraine tace ana kashe mata sojoji 100 kowacce rana

Kasar Ukraine tace tana asarar sojoji akalla 100 da ake kasha mata kowacce rana a yakin da take fafatawa da Rasha wadda ta kaddamar da mamayen karbe iko da kasar tun daga watan Fabarairu, yayin da akalla 500 ke samun raunuka.

Wasu daga cikin dakarun Ukraine a wani asibiti
Wasu daga cikin dakarun Ukraine a wani asibiti AP - Bernat Armangue
Talla

Ministan tsaron kasar Oleksiy Reznikov ya bayyana haka inda yake cewa halin da ake ciki a bakin dagar da ake musayar wuta tsakanin bangarorin biyu na da matukar wahala.

Reznikov yace sojojin Rasha na ci gaba da jajircewa da kuma kutsawa, yayin da dakarun Ukraine ke nuna tirjiya abinda ya sa ake kashe musu sojoji akalla 100 kowacce rana, bayan kusan 500 da suke samun raunuka.

Shugaba Volodymyr Zelensky yace makomar Donbas wadda ke dauke da masana’antu na tattare da samun nasarar da dakarun su za suyi a Severodonetsk wanda tuni dakarun Rasha suka kwace iko da akasarin sa.

A jawabin da ya yiwa jama’ar kasar yammacin jiya, Zelensky ya bayyana fafatawar a matsayin mafi wahala daga cikin yakin da dakarun kasar keyi.

Gwamnan Lugansk Sergiy Gaiday ya bayyana cewar dakarun Ukraine zasu kwato birnin Severodestsk a cikin kwanaki 2 zuwa 3 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.