Isa ga babban shafi

Karancin makamashi zai tilastawa G7 jinkirta shirin yaki da dumamar yanayi

Shugabannin kasashe 7 mafi karfin tattalin arziki a duniya da aka fi sani da G7, sun ce akwai yiyuwar jinkirta wasu daga cikin alkawurran da suka dauke don yaki da dumamar yanayi a duniya.

Taron kasashen G7 a Jamus.
Taron kasashen G7 a Jamus. AP - Markus Schreiber
Talla

Manyan kasashen na matsayin 'yan gaba-gaba da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yanayi ta Paris da ke da kudirin rage gurbataccen tiririn da masana'antu ko kuma wasu nau'ikan makamashi ke fitarwa da nufin ceto duniya daga barazanar dumamar yanayin da tuni aka fara ganin illarta.

Wani daftarin da shugabannin kasashen 7 da suka kunshi Amurka da Jamus, Birtaniya da Faransa kana Italiya da Canada da kuma Japan suka amince da shi, na nuni da cewa za su ci gaba da bayar da kudade domin hakar wasu nau'ikan makamashin da ke taimakawa wajen gurbata muhalli.

Matakin kasashen 7 na zuwa ne a dai dai lokacin da duniya ke fuskantar karancin makamashi sanadiyyar rikicin Rasha da Ukraine, wanda tuni ya sanya wasu kasashe karkatawa amfani da makamashin gawayi maimakon gas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.