Isa ga babban shafi

Yawan al'ummar duniya zai kai biliyan 8 a watan Nuwamba

Ana sa ran yawan al’ummar duniya ya kai biliyan 8 a ranar 15 ga watan Nuwamban wannan shekarar, kamar yadda hasashen da majalisar dinkin duniya ta yi a wannan Litinin ya nuna.

Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya António Guterres.
Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya António Guterres. AP
Talla

Hasashen ya nuna cewa india za ta zarce China a yawan Jama’a a cikin shekarar 2023.

Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya ce wannan ci gaba da aka samu a bangaren yawan jama’a, tuni ne a kan hakkin da ya rataya a kan al’ummar duniya wajen kula da muhali da yanayi, sannan kuma lokaci ne na nazari a kan inda aka gaza wajen kulawa da juna.

Hasashen da hukumar kulada tattalin arziki da zamantakewa ta majalisar dinkin duniya ta yi ya nuna cewa a karon farko tun bayan shekarar 1950 yawan al’ummar duniya ba ya karuwa cikin sauri.

Rahoton hasashen ya ce yawan al’ummar duniya na iya kai wa biliyan 8 da rabi a shekarar 2030, da biliyan 9 da miliyan dari 7 a 2050, inda daga nan zai tsaya a inda yake har zuwa karni na 22.

A yayin da kasashe masu tasowa da dama ke bin tsarin takaita haihuwa, fiye da rabin  karuwar  yawan al’umma zai kasance ne a kasashe maso tasowa 8, wato, Jamhuriyar dimokaradiyya Congo, Masar, Habasha, India, Najeriya, Pakistan, Philippines da Tanzania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.