Isa ga babban shafi

Jirgin kayan abinci na farko ya bar Ukraine zuwa kasuwar Duniya- MDD

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sanar da fara jigilar kayan abinci daga tashoshin jiragen ruwan Ukraine zuwa sauran sassan duniya, a matsayin wani gagarumin ci gaba a kokarin da ake yi wajen shawo kan hauhawar farashin kayan abinci da takin zamani a duniya.

Wani jirgin ruwa daga tashar Odessa.
Wani jirgin ruwa daga tashar Odessa. via REUTERS - OLEKSANDR KUBRAKOV/ UKRAINE MINI
Talla

Guterres dai na gabatar da jawabi ne jim kadan bayan da jirgin farko dauke da abinci ya tashi daga tashar ruwan Odessa da ke Ukraine bayan share tsawon watanni da dama karkashin mamayar kasar Rasha.

A cewar Guteress matakin da aka cimma wani muhimmin ci gaba la'akari da yadda hakan zai bai wa tarin jiragen ruwan kasuwanci damar isar da kayayyakin abinci da kuma samar da daidaito a kasuwannin abinci na duniya.

Yarjeneniyar jigilar abinci daga tekun Bahar Assawad dai wata dama ce ta jigilar abinci daga tashoshin ruwa uku na Ukraine wato Odessa da Chorhomask da kuma Uzny.

Babban magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ya ce dukkaninmu bangarorin sun amince da fitar da kayayyakin abinci da kuma takin zamanin da Rasha ke samarwa zuwa kasuwar duniya, matakin da zai kawo sauki a game da tsada da kuma hauhawar farashin da ake fama da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.