Isa ga babban shafi

Amurka na kwadayin musayar fursunoni da Rasha

Rasha da Amurka na ci gaba da tattaunawa game da musayar fursunoni, dai-dai lokacin da tashe-tashen hankula ke kara ta'azzara kan kutsawar sojan kasar a Ukraine.

Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan da takwaransa na Amurka Joe Biden
Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan da takwaransa na Amurka Joe Biden AP - Patrick Semansky
Talla

Wani dillalin makamai na kasar Rasha, kuma tsohon malami da kuma fitacciyar ‘yar kwallon kwando na Amurka na daga cikin wadanda za a iya yin musanya da su.

- Brittney Griner-

Fitacciyar ‘yar kwallon kwando ta Amurka Brittney Griner na fuskantar shari'a a Rasha bayan da aka kama ta a filin jirgin sama na Moscow a watan Fabrairu bisa laifin mallakar man wiwi. Kamen ya zo ne kwanaki kadan kafin Moscow ta kaddamar da farmaki a Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu.

Sai dai ta yiwa jami’an kasar bayanin cewa, wani likitan Amurka ne ya rubuta mata shi a matsayin maganin rage radadin raunukan da ta samu.

‘Yan wasan mai shekaru 31 ta shiga Rasha ne domin buga kwallon kwando a wata kungiya da ke Yekaterinburg ta kasar Rasha a lokacin hutun kakar wasa.

An tuhumi ‘yar wasan da ta lashe lambar zinare sau biyu a gasar Olympics kuma zakarar NBA ta mata da laifin safarar miyagun kwayoyi sannan kuma masu gabatar da kara na Rasha sun bukaci a yanke mata hukuncin shekaru tara da rabi a gidan yari.

- Paul Whelan –

An kama tsohon ma'aikacin ruwan Amurka Paul Whelan mai shekaru 52 a watan Disambar 2018 kuma jami'an tsaron Rasha sun zarge shi da laifin leken asiri.

An tsare shi ne a ziyarar da ya kai birnin Moscow don halartar wani bikin aure lokacin da ya dauki na’urar adana bayanai ta USB, domin adana hotunan bikin da ya halarta.

An yankewa tsohon jami'in tsaron wanda kuma ke da fasfo din Burtaniya, Canada da Ireland hukuncin daurin shekaru 16 kan laifin leken asiri a watan Yunin 2020.

A lokacin da yake fuskantar tuhuma a gaban kotu, Whelan ya dage cewa ba shi da laifi.

- Marc Fogel –

A watan Yuni ne aka yanke wa wani malami a wata makaranta da ke birnin Moscow, kuma dan kasar Amurka, mai suna Marc Fogel, hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari, bisa tuhumarsa da laifin safarar wiwi.

Jami'an kwastam na Rasha sun ce sun gano tabar wiwi da man hash a cikin kayan Fogel lokacin da ya isa kasar daga birnin New York.

Fogel ya ce likitoci ne suka rubuta masa maganin tabar wiwi daga Amurka bayan an yi masa tiyatar kashin baya.

Rasha dai ta haramta amfani da taba ko kuma ganyen wiwi a matsayin magani.

Jami'an Rasha sun ce Fogel yana aiki a ofishin jakadancin Amurka da ke Moscow tun da farko kuma yana cin gajiyar kariya ta diflomasiya har zuwa watan Mayu 2021.

- Victor Bout –

A shekara ta 2012 ne aka yankewa dan kasar Rashan nan Victor Bout hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari a Amurka bayan da aka zarge shi da baiwa ‘yan tawaye makamai a wasu tashe-tashen hankula mafi muni da suka auku a wasu kasashe.

Victor Bout  mai shekaru 55 ana kallon sa a matsayin fitaccen dan kasar Rasha da aka daure a Amurka.

An kama tsohon jami'in sojan sama na Tarayyar Soviet kuma kuma masanin harsuna a Thailand a shekara ta 2008 yayin wani samame da jami'an Amurka suka yi a kan 'yan tawayen FARC na Columbia da ke neman makamai.

Masana dai na ganin cewa, ya kwaikwayi wani fim din Amurka mai suna “Lord of War” da aka yi a shekarar 2005 da ke nuna yadda ake  safarar makamai ga kasashen Angola da Laberiya da yaki ya daidaita.     

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.