Isa ga babban shafi

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki tsakanin Islamic Jihad da Isra'ila a Gaza

Kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da kungiyar mayakan Islamic Jihad a yankin Falasdinu ta fara aiki a safiyar yau litinin, lamarin da ya sa ake bayyana fatan cewa mumunan rikicin da ya barke kwanan nan, har ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 44, ciki har da kanan yara 15 ya zo karshe.

Wasu yankuna da Isra'ila ta yiwa luguden wuta a yankin na Falasdinu.
Wasu yankuna da Isra'ila ta yiwa luguden wuta a yankin na Falasdinu. REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA
Talla

An cimma wannan yarjejeniyar, wadda ta fara aiki a hukumance da karfe 8 da rabi na daren lahadi agogon GMT ne da zummar kawo karshen rikici mafi muni a yankin zirin Gaza tun bayan yakin kwanaki 11 da ya jijjiga yankin na Falasdinawa a shekarar da ta gabata.

Ko da ya ke an dan kai hare hare da rokoki gabanin, da kuma jim kadan bayan cimma yarjejeniyar, babu rahoton saba ka’ida daga dukkan bangarorin ya zuwa yanzu.

A wata sanarwa da ta aike ‘yan mintoci bayan cimma yarjejeniar tsagaita wutar, rundunar sojin Isra’ila ta ce tana luguden wuta a wasu wuraren da ‘yan kungiyar Islamic Jihad su ke ne a matsayin martani ga harin da aka kai yankinta.

A yayin da dukkannin bangarorin suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta wadda Masar ta bijiro da ita, kowannen su ya yi gargadin mayar da martani mai zafi ga duk wanda ya saba.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi na’am da tsagaita wutar, ya na mai gode wa shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi sakamakon rawar da kasar sa ta taka wajen bijiro da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.