Isa ga babban shafi

Yau Taliban ke cika shekara guda da karbe mulkin Afghanistan

Yau ake cika shekara guda da kwace ikon da kungiyar Taliban ta yi a kasar Afghanistan, abin da ya kawo karshen mulkin zababbiyar gwamnatin Ashraf Ghani da kuma kawar da dimokiradiyar da Amurka ta kafa na kusan shekaru 20 bayan mamaye kasar.

Wasu daga cikin jagororin Taliban
Wasu daga cikin jagororin Taliban © AP - Alexander Zemlianichenko
Talla

A ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2021, mayakan kungiyar Taliban suka kutsa kai cikin birnin Kabul, fadar gwamnatin kasar, shekaru 20 bayan kawar da su da sojojin Amurka suka yi sakamakon harin ta’addancin da aka kai birnin New York da ake kira harin 11 ga watan Satumba.

Bayan karbe ikon da Taliban ta yi a rana mai kamar ta yau, hukumomi da kasashen duniya sun katse hulda da kasar da kuma dakile kudaden da suke taimaka wa Afghanistan da shi, abin da ya jefa kusan daukacin jama’ar kasar cikin talauci da kuma yunwa saboda rashin samun abinci mai gina jiki.

Ya zuwa yanzu babu wata kasa a duniya da ta yi shelar amincewa da gwamnatin Taliban, yayin da shugabannin kasar suka karya alkawarin da suka yi na sassauta yadda suke iko da bai wa mata yancin aiki da bai wa 'yan mata damar zuwa makaranta.

Masana na danganta karbe ikon Taliban da yarjejeniyar da ta kulla da wakilan gwamnatin Amurka a karkashin shugaba Donald Trump ranar 29 ga watan Fabairun shekarar 2020 na ganin an janye dakarun kasar daga ranar 1 ga watan Mayun bara.

Kungiyar Taliban da ta yi alkawarin dakatar da kai hare-hare, ta zafafa hare-harenta a kan dakarun Afghanistan inda ta rika samun galaba a kansu saboda janyewar sojojin Amurka da ke taimaka musu.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2021, shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewar, kasar za ta janye sojoji 2,500 zuwa 3,500 da suka rage a kasar kafin ranar 11 ga watan Satumbar bara, kuma wannan sanarwa ta dada bude wa Taliban kofar ci gaba da kai hare-hare da kuma kama garuruwa, inda kafin watan Agusta ta kama akasarin manyan biranen kasar.

A ranar 15 ga watan Agusta, mayakan kungiyar suka yi tattaki zuwa cikin birnin Kabul bayan tserewar shugaba Ashraf Ghani wanda ya gudu ya bar kasar, yayin da a ranar 16 ga wata dubban fararen hular kasar suka mamaye tashar jiragen saman Kabul inda suke neman gudu domin kauce wa zama a karkashin mulkin Taliban.

A ranar 18 ga watan Agusta, mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya yi alkawarin cewar mayakan kungiyar ba za su rama hare-haren da sojojin gwamnati suka kai musu ba, yayin da ya yi alkawarin cewar za su bai wa mata damar yin aiki da karatu kamar yadda addinin Islama ya tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.