Isa ga babban shafi

Zagon-kasa ne ya haddasa gobara a ma'ajiyar makamanmu - Rasha

Ma’aikatar Tsaron Rasha ta bayyana cewa, zagon-kasa ne ya haddasa tashin wutar da ta haifar da fashe-fashen bama-bamai a wurin adana makamanta da ke yankin Crimea da Moscow ta mamaye.

Wasu daga cikin sojojin Rasha da aka jibge a Ukraine
Wasu daga cikin sojojin Rasha da aka jibge a Ukraine AFP - ALEXANDR BOGDANOV
Talla

Wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron Rasha ta fitar ta ce, a safiyar ranar 6 ga watan Agusta da muke ciki, aka lalata mata wurin ajiyar makaman sojinta da ke kusa da kauyen Dzhankoi a sanadiyar zagon-kasa.

Kazalika akwai tarin kayayyakin amfani na fararen hula da suka  lalace  da suka hada da turakun wutar lantarki da tashar samar da wutar da layin dogo har ma da wasu gidajen al’umma, amma babu wani mummunan rauni da aka samu kamar yadda sanarwar ta yi karin haske.

Hotunan da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda manyane dunkulen wuta ke lulawa sararin samaniya  a wurin ajiyar makaman, yayin da bakin hayaki ya turmuke ko ina.

Gwamnan Crimea da Moscow ta nada, Sergei Aksyonov da ya ziyarci wurin ajiyar makaman, ya ce, fararen hula biyu ne kacal suka samu rauni kuma ba sa fuskantar hatsarin rasa rayukansu.

Hukumomin Rasha sun ce, an sauya wa wasu mutane dubu 2 mahallansu sakamakon gobarar a ma’ajiyar makaman ta sojin Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.