Isa ga babban shafi

Ba za mu yi zaman lafiya da Rasha ba - Ukraine

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya soke duk wani batun zaman lafiya tsakaninsa da Rasha har sai ta janye dakarunta daga kasarsa.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky. AP
Talla

Kalaman Zelensky na zuwa ne jim kadan da ganawar da ya yi da takwaransa na Turkiya, Recep Tayyip Erdogan da kuma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres da suka kai masa ziyara.

Zelensky ya  shaida wa manema labarai cewa, lallai ya yi mamakin abin da ya ji daga Erdogan wanda ya ce masa,  Rasha ta shirya karbar zaman lafiya, amma a cewar shugaban na Ukraine, babu yadda hakan zai yiwu har sai Rashar ta fara kwashe sojojinta daga kasar kafin su yi nazari kan amincewa da bukatarta ko kuma akasin haka.

Tuni dai Erdogan ya bayyana goyon bayansa ga Ukraine, matakin da ke zuwa makwannni biyu da tattaunawar da ya yi  shugaban Rasha Vladimir Putin kan wasu batutuwa da suka hada da bunkasa tattalin arzikin kasashensu.

Shugaba Erdogan ce, Turkiya wadda mamba ce a kungiyar tsaro ta NATO, na nan daram a gefen Ukraine, sannan za ta ci gaba da kokakarin lalubo hanyoyin diflomasiya domin kawo karshe fadan da ake gwabzawa tsakanin kasashen biyu.

Ganawarsa da Zelensky na zuwa ne a daidai lokacin da hankalin duniya ya tashi saboda fadan da ake gwabzawa a zagayen tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia.

Tashar dai yanzu haka na hannun dakarun Rasha da suka mamaye ta, yayin da take shan luguden wuta, abin da ya sa shugaba Erdogan ya yi gargadin sake aukuwar musibar Chernobyl da aka gani a shekarar 1986.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.