Isa ga babban shafi

Fafaroma zai nada limaman majami'a 20 da za a zabi magajinsa a ciki

Shugaban darikar Katolika na Duniya, Fafaroma Francis, wanda a kwanan nan ya bayyana yiwuwar yin murabus saboda tabarbarewar lafiyarsa, zai nada manyan limaman majami'a guda 20 a ranar Asabar, wadanda ake sa ran daga cikinsu ne za a zabi magajinsa wata rana.

Zaman rantsar da limaman majami'ar Katolika.
Zaman rantsar da limaman majami'ar Katolika. AP
Talla

Sabbin Limaman da ake kira da Cardinals a Turance sun fito ne daga kasashen da suka hada da Brazil da Najeriya, da India, sai Singapore da kuma Gabashin Timor.

Francis, wanda ya soke gudanarwa ko kuma halartar taruka da dama a cikin 'yan watannin, a yanzu haka ya koma amfani da keken guragu saboda ciwon gwiwa da yake fama da shi, abinda ya sanya shi a watan da ya gabata bayyana cewa, kofa a bude take ya sauka.

Dokar hana fitar da kungiyar IPOB ke tilastawa mazauna yankin kudu maso Gabashin Najeriya a kowace ranar litiinin, ya gurgunta harkokin kasuwanci da ayyukan hukuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.