Isa ga babban shafi

Ukraine ta ce ta fara kai farmaki domin kwato kudancin kasar da ke hannun Rasha

Ukraine ta sanar da fara kai farmakin da aka dade ana jira domin kwato yankunan kudancin kasar da sojojin Rasha suka kwace tun bayan mamayar da suka yi watanni shida da suka gabata, matakin da ke nuna kwarin gwiwar da Kyiv ke da shi yayin da taimakon sojan kasashen yammacin duniya ke kara tasiri.

Ukraine ta kasance tana amfani da makamai da kasashen Yamma ke kai mata wajen kai hari kan dakarun Rasha.
Ukraine ta kasance tana amfani da makamai da kasashen Yamma ke kai mata wajen kai hari kan dakarun Rasha. AFP - OLEKSANDR GIMANOV
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata tawaga daga hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta nufi kasar Ukraine domin duba tashar nukiliyar Zaporizhzhia da sojojin Rasha suka kame a watan Maris, amma har yanzu hukumomin Ukraine ne ke tafiyar da su wanda ya kasance abu mafi daukar hankali a yakin.

Rasha da Ukraine dai sun yi musayar zarge-zargen harba makamai masu linzami a kusa da tashar nukiliyar, mafi girma a Turai, a daidai lokacin da ake fargabar  burbushin magadisu a kasar zai haifar da bala'I irin na Chornobyl da ya faru a 1986.

"A yau mun fara munanan ayyuka ta bangarori daban-daban, ciki har da yankin Kherson," in ji mai magana da yawun rundunar sojojin kasar Natalia Humeniuk.

Rasha ta yi saurin kame yankunan kudancin Ukraine da ke kusa da gabar tekun Black Sea, ciki har da birnin Kherson, a farkon yakin da aka yi, sabanin yunkurin da ta yi na kwace babban birnin kasar Kyiv.

Ukraine ta kasance tana amfani da makamai da kasashen Yamma ke kai mata, wajen kai hari kan dakarun Rasha.

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kuma Ukraine sun yi kira da a janye kayan aikin soji da kuma dakaru daga cibiyar Nukiliyar don tabbatar da cewa ba a kai hari wurin ba.

Hakan ta sanya mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova, ta ce dole ne hukumar kula da makamashi ta duniya IAEA ta gudanar da aikinta ba tare da sanya siyasa a ciki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.