Isa ga babban shafi

Yau ake jana'izar tsohon shugaban Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev

Yau Asabar ake jana’iza da kuma bankwanar karshe ga gawar tsohon shugaban Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev, jajirtaccen da ya kawo karshen yakin cacar baka tsakanin manyan kasashen Duniya, wanda kuma a hannunsa ne tarayyar ta Soviet mafi girma a baya ta rushe zuwa daidaikun kasashe.

Jana'izar tsohon jagoran tarayyar Soviet Mikhaïl Gorbatchev.
Jana'izar tsohon jagoran tarayyar Soviet Mikhaïl Gorbatchev. AFP - EVGENIA NOVOZHENINA
Talla

Tuni dai aka ga dandazon mutane a dakin taro na Hall of Coloums inda suke ajje furanni da kalaman ban girma ga jajirtaccen shugaban da ake ganin shi ya samar da cikakken ‘yanci ga ‘yan kasar.

Tun da sanyin Safiya aka sanya kade-kaden jana’iza a dakin taron wanda anan ne ake jana’izar fitattun shugabannin Rasha da suka mutu ciki har da Joseph Stalin da ya mutu a shekarar 1953.

Bayan kammala jana’izar a yau asabar za a birne Gorbachev a makabartar Novodevichy inda ake birne mashahuran jagororin kasar, yayinda za a yi masa kabari gusa da matarsa Raisa da ta mutu a shekarar 1999.

Shugaba Vladimir Putin dai baya daga cikin wadanda za su halarci jan’izar ta yau saboda rashin lokaci kamar yadda fadar Kremlin ta sanar tun a shekaran jiya alhamis.

Sai dai bayanai sun ce tun a larabar da ta gabata, shugaba Putin ya yi bankwanar karshe da gangar jikin Gorbachev inda gidajen talabijin din kasar suka hasko wani faifan bidiyo da shugaba Putin ke ajje fure a gaban akwatin gawar Gorbachev da aka ajje a dakin taron na Hall of Columns tun a sa’o’I kalilan gabanin mutuwarsa inda kuma ya yi shirun ‘yan mintuna don girmama jagoran na Soviet.

Haka zalika bidiyon ya nuna Putin ya dukar da kansa alamun girmamawa tare da yin alamar gicciye bayan dagowarsa duk dai a matsayin girmamawa da kuma bankwanar karshe ga jagoran na tsohuwar tarayyar Soviet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.