Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci tsaurara tsaro a tashar nukiliyar Ukraine

Hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a kafa wani yanki na tsaro a kewayen tashar nukiliyar Zaporizhzhia ta kasar Ukraine, wadda ke karkashin ikon Rasha.

Wani yanki na tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia da ke kasar Ukraine kenan
Wani yanki na tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia da ke kasar Ukraine kenan REUTERS - ALEXANDER ERMOCHENKO
Talla

Dakarun Rasha sun kwace iko da cibiyar makamashin nukiliya mafi girma a Turai a farkon watan Maris, kuma an sha kai hare-hare a kusa da wajen, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar bala'in nukiliya, yayin da bangarorin biyu ke zargin juna da harin da aka kai kan cibiyar.

Halin da ake ciki a yanzu ba zai yuwu ba, in ji Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (IAEA) a cikin wani rahoto bayan da ta aike da tawagar jami'ai zuwa cibiyar a makon da ya gabata.

Akwai bukatar daukar matakan gaggawa  na wucin gadi don hana afkuwar hatsarin nukiliyar da ya taso sakamakon wani harin soji," in ji hukumar ta IAEA.

"Hukumar IAEA ta ba da shawarar a dakatar da harba bama-bamai a wurin da kuma kewayen cibiyar nan take domin kaucewa wata barna ga wurin da kayayyakin da ke ajiye."

Jami'in da Moscow ta ajiye a Zaporizhzhia Vladimir Rogov ya soki ra'ayin samar da tsaro, yana mai cewa a maimakon haka abin da ake bukata don kare martabar cibiyar shi ne yarjejeniyar aiwatar da tsagaita wuta.

Kwamishinan kare hakkin dan adam a majalisar dokokin Ukraine Dmytro Lubinets ya ce rahoton "kusan ba ya kula da gaskiyar da ke da alaka da tsaron lafiyar ma'aikata da kuma laifukan yaki da ma'aikatan Rasha suka aikata dangane da ma'aikatan tashar nukiliyar: kisan kai. azabtarwa, kamawa ba bisa ka'ida ba da kuma gurfanar da masu laifi, da sauransu".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.