Isa ga babban shafi

Sabon Sarkin Ingila ya yi wa al'umma jawabinsa na farko

Sarki Charles na 3 ya yi wa mutanen Birtaniya jawabi ta kafar talabijin, kwana guda bayan ya maye gurbin mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth ta biyu, wadda ta rasu jiya tana da shekaru 96 a duniya.

Sarki Charles na uku
Sarki Charles na uku © Yui Mok, AP
Talla

Yayin jawabinsa, Sarkin ya bayyana aniyarsa ta dorawa daga inda mahaifiyarsa ta tsaya, inda yake cewa.

An goya ni ta yadda zan mutunta aiki tukuru ga sauran jama’a da kuma girmama mutane, ta hanyar al’ada da 'yanci da nauyin tarihinmu mai matukar tasiri da kuma tsarinmu na mulkin Firaminista. Kamar yadda Sarauniya da kanta ta jajirce, ni ma yanzu zan yi haka, a sauran lokacin da Allah ya bani, wajen mutunta kundin tsarin mulki da ke da tasiri a kasarmu.

 

Ga mahaifiyata mai matukar daraja, yayin da kika fara tafiyarki ta karshe mai muhimmanci, domin kaiwa ga mahaifina da ya riga ki, ina so na shaida miki wannan a takaice, na gode. Na gode da kaunar da kika nuna min, da sadaukarwarki ga iyalanmu da kuma iyalan kasashen da kika yi wa aiki tukuru a wadannan shekaru masu yawa. Ina fata jiragen malaiku za su kaiku wurin hutu.

 

Takaitaccen tarihin Sabon Sarkin na Ingila

An haifi Sarki Charles na uku ne a ranar 14 ga watan Nuwambar shekarar 1948 a fadar Buckingham inda aka rada masa suna Yarima Charlse Philip Arthur George.

A ranar 15 ga watan Disambar shekarar 1948  limamin Kirista, ko kuma Archbisop na Kantabori ya masa batisma, yayin da kakansa kuma Sarki George na 6 ya rasu a ranar 6 ga watan Fabarairu na shekarar 1952, abin da ya bai wa mahaifiyarsa damar hawa karagar mulki, kana shi kuma ya zama Yarima mai jiran gado.

An yi bikin nada mahaifiyarsa Elizabeth a ranar 2 ga watan Yunin shekarar 1953, yayin da ya fara karatu a makarantar Gordonstoun a arewa maso gabashin Scotland, inda mahaifinsa Yarima Philip ya yi karatu.

Sarki Chales na uku ya yi aikin sojan ruwa a shekarar 1971, kamar yadda mahaifinsa ya yi, a shekarar 1974 kuma ya yi aiki da jiragen saman yakin kasar.

A 1976 ya zama kwamandan sojin ruwan Birtaniya.

Ya auri Diana wadda ta haifa masa yaya biyu wato Yarima William da Yarima Harry, kafin su rabu ta kuma rasu a hadarin mota, kuma ya auri tsohuwar budurwarsa Camilia.

Yarima Charles ya zama Sarki Charles na uku sakamakon rasuwar mahaifiyarsa a wannan Alhamis din, yana da shekaru 73.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.