Isa ga babban shafi

Mutane miliyan 50 na cikin kangin bauta da azabtarwa a sassan Duniya- MDD

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane miliyan 50 ne ke cikin kangin sabon salon bautarwa na zamani da kuma azabtarwa da auren dole a fadin duniya, yayin da ta yi gargadin cewa adadin ka iya karuwa cikin hanzari matukar ba’a yi hattara ba.

Bayan dogon bincike ne Majalisar dinkin duniya ta tabbatar da yadda miliyoyin mutane ke cikin halin kangin bauta.
Bayan dogon bincike ne Majalisar dinkin duniya ta tabbatar da yadda miliyoyin mutane ke cikin halin kangin bauta. REUTERS/Costas Baltas
Talla

Majalisar dinkin duniyar dai ta ayyana wani kuduri na dakatar da irin wannan bauta a fakaice nan da shekarar 2030, sai dai kuma maimakon adadin ya ragu karuwa ma yake yi kamar wutar daji, tana mai cewa mutane miliyan 10 ne suka gamu da auren dole tsakanin shekarun 2016 zuwa 2021.

Majalisar dinkin duniyar ta kuma ce mutum daya cikin mutane 150 na fuskantar irin wannan bautarwa ko ta auren dole, ko cin zarafi, ko kuma aikin karfi musamman ga kananan yara da sauran matsaloli.

Rahoton hukumar kula ayyuka da kaurar jama’a ta Majalisar dinkin duniya da hadin gwiwar zauren Walk Free ya kuma ce a karshen shekarar da ta gabata, mutane miliyan 28 a duniya na fuskantar aikin wahala bisa dole yayin da mutane miliyan 22 ke cikin auren dole.

Hukumar ta kuma kara da cewa cutar Covid-19 ta kara ingiza matsalar tare da kara jefa al’umma cikin matsanancin talauci da cin bashi ga ma’aikata.

Hukumar ta kuma kara da cewa wannan ya ta’azzara matsalar cin zarafin jama’a da kuma bautar da yara da tilasta musu aikin da ya fi karfin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.