Isa ga babban shafi

Amurka na neman dan Najeriyar da ya damfare ta Dala miliyan 30

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI na farautar wani dan asalin kabilar Igbo a Najeriya bayan ya damfari gwamnatin New York kudaden da yawansu ya zarta Dala miliyan 30, kwatankwacin Naira biiliyan 15.

Wasu daga cikin jami'an hukumar FBI ta Amurka.
Wasu daga cikin jami'an hukumar FBI ta Amurka. ©Reuters
Talla

Wata sanarwa da ofishin babban lauyan gwamnatin Amurka ta fitar ta ce, ana tuhumar Chidozie Collins Obasi mai shekaru 29 kan aikata laifuka da dama da suka hada da damfara ta hanyar amfani da sakwannin yanar gizo.

A farko-farkon barkewar annobar Covid-19 , Obasi ya yi ta sayar wa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na Amurka na’urar numfashi ta bogi, kafin daga bisani ya saci bayanan wani Ba’amurike, inda ya yi ta karbar kudaden rage radadin cutar Covid-19 da sunansa.

Hukumomin Amurka sun ce, Obasi ba shi kadai ba ne yake aikin damfarar domin kuwa yana da wasu mataimaka a kasar Canada, amma daga Najeriya yake gudanar da na shi ayyukan na damfarar.

Mudddin dai FBI ta yi nasarar cafke shi, Obasi ka iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 621 da kuma cin sa tarar Dala miliyan 5 da dubu 750.

Kazalika hukumomin na Amurka za su tilasta masa maido da daukacin kudaden da ya sace da suka zarta Dala miliyan 31.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.