Isa ga babban shafi

Kwararru sun bayar da shawarar karkata abincin dabbobi zuwa ga mutane

Wani binciken kwararru ya bayyana cewar, karkatar da hatsi da sauran nau’ikan abincin da ake ciyar da dabbobi zuwa ga amfanin dan adam, na iya samar da wadataccen abincin da zai ciyar da karin mutane biliyan daya a duniya.

Abinci dangin hatsi da akan yi amfani da shi wajen ciyar da dabbobi a Turai.
Abinci dangin hatsi da akan yi amfani da shi wajen ciyar da dabbobi a Turai. © REUTERS/Hannibal Hanschke/File Photo
Talla

Akasarin dabbobi da kifayen da ake kiwonsu dai ana ciyar da su ne da nau’ikan abinci irin su hatsi, wadanda a lokaci guda suke zama cimaka ga dan adam.

Yayin da duniya ke fafutukar ciyar da daruruwan miliyoyin mutane da abinci mai gina jiki don kula da lafiyarsu, masu bincike a kasar Finland sun yi nazariin cewar karkatar da abincin da ake biwa dabbobi zuwa ga mutane hanya ce mafi sauki ta magance matsalar.

Masanan sun yi nazarin bayanan tsarin abinci na duniya,  inda suka mayar da hankali kan wadatar sauran hanyoyin abinci ga dabbobi, wadanda akan iya samar da su ta hanyoyin noma sabanin abincin dan Adam kai tsaye.

Kusan kashi 15 cikin 100 na fiye da tan biliyan shida na abincin da dabbobi ke cinyewa kowace shekara sun kunshi abubuwan da dan Adam zai iya amfani da su a matsayin abincinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.