Isa ga babban shafi

Kasashen yamma na zargin Rasha da kai hari kan bututun gas

Ukraine ta zargi Rasha da haddasa yoyon wasu manyan bututun iskar gas biyu da ke zuwa Turai a wani harin da ta bayyana a matsayin na ta'addanci.

Yadda gas ke fitowa daga Nord Stream 2 a saman tekun Baltic
Yadda gas ke fitowa daga Nord Stream 2 a saman tekun Baltic © REUTERS
Talla

Mai ba shugaban kasar Ukraine shawara Mykhaylo Podolyak ya ce barnar da aka yi wa Nord Stream na 1 da kuma 2 wani mataki ne na zalunci ga Tarayyar Turai.

Ya ce Rasha na son haifar da rudani a nahiyar kafin zuwan lokacin hunturu, don haka ya bukaci kungiyar EU da ta kara tallafin soji ga Ukraine don ci gaba da yakar Rasha.

Tuni dai wasu daga cikin shugabannin Turai suka fara tsokaci kan lamarin inda suke ganin da gangan Rasha ta aikata hakan.

Fira ministan Poland, Mateusz Morawiecki ya ce ba komai ya harfar da hakan ba face zagon kasa inda yake kallonsa a matsayin abinda ke da alaka da yakin Ukraine.

Itama fira ministan Denmark, Mette Frederiksen, ta ce da sauran lokaci kafin yanke hukunci akan abinda ya haifar da yoyon iskar gas din, amma abu ne mai wuya a iya gano abinda ya haifar da hakan lokaci guda.

Wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce ba za su yi hasashe kan dalilin faruwar lamarin ba, amma a shirye kasar ta ke ta goyi bayan kokarin da kasashen Turai ke yi na bincike a kai.

A baya dai kungiyar ta EU ta zargi Rasha da yin amfani da damar ta wajen rage yawan iskar gas din da take saida mata, a wani martani da ta ke maidawa game da takunkumin da kasashen Yammaci suka kakaba mata saboda mamayar da ta yi wa Ukraine.

Sai dai Moscow ta musanta zargin ta da ake yi, tana mai cewa takunkumin da a ka sanya mata ne ya sa ba ta iya kula da bututun iskar gas din yadda ya kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.