Isa ga babban shafi

Dubban mazaje Rasha ta tura gida saboda rashin cancantar shiga aikin soja

Dubban 'yan kasar Rasha da aka yi gangamin dauka aikin soji an mayar da su gida, sakamakon gaza cancantar shiga aikin, koma baya na baya-bayan nan da shugaba Vladimir Putin ya samu na daukar ma'aikata 300,000 a aikin soja.

Hukumomin kasar sun ce bisa gwajin da aka yi da dama ba za u iya shiga aikin soja ba
Hukumomin kasar sun ce bisa gwajin da aka yi da dama ba za u iya shiga aikin soja ba AP - Andrew Kravchenko
Talla

Mikhail Degtyarev, gwamnan yankin Khabarovsk a gabas mai nisa na Rasha, ya ce dubban maza ne aka bayar da rahoton cewa sun shiga cikin tsarin, kwanaki 10 da fara dauka amma da yawa ba su cancanta ba.

Ya ce an cire kwamandan soji a yankin Khabarovsk na Rasha, amma korar tasa ba za ta yi tasiri ba.

Kiran farko da Rasha ta yi na neman karin dakaru tun bayan yakin duniya na biyu, wanda aka ayyana a ranar 21 ga Satumba, ya haifar da rashin gamsuwa da tserewar dubban mazaje zuwa kasashen waje.

Sai dai hukumomin kasar sun ce matakin ya shafi wadanda ke da kwarewa kuma za su iya bada gudun mowa sosai ga aikin soja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.