Isa ga babban shafi

Kungiyoyin kare muhalli fiye da 100 za su halarci taron yanayi a Masar

Kungiyoyin fararen hula fiye da 100 daga kasashen Afirka na shirin yin tattaki zuwa Masar, domin gabatar da kiran hadin gwiwa kan bukatar kara daukar matakan magance matsalar Dumamar yanayi, a yayin babban taron da zai gudana kan sauyin yanayi nan da ‘yan makwanni.

Tuni dai aka fara ganin illar dumamar yanayi musamman a kasashen Afrika.
Tuni dai aka fara ganin illar dumamar yanayi musamman a kasashen Afrika. None - PASCAL ROSSIGNOL
Talla

Tawagar kungiyoyin fararen hular masu rajin kare muhalli, za ta yada zango ne a birnin Dakar, da kuma Kinshasa, inda wasu tarukan sharar fage kan matsalar Sauyin Yanayi ke gudana.

Daga cikin muhimman batutuwan da babban taron Sauyin Yanayin a nahiyar Afirka zai mayar da hankali akai, sun hada da kare hakkokin manoma gami da daukar matakan hana gurbatar muhalli, da tabbatar da baiwa mata da matasa damar samun wakilci, a yayin aiwatar da matakan da aka bayar da shawarar dauka.

Wani muhimmin batu kuma shi ne kira ga kasashe masu arziki da su cika alkawarin da suka dauka yayin taron sauyin yanayi a shekarar 2015, na tallafawa kasashe masu tasowa da dala biliyan 100 duk shekara har zuwa shekarar 2025, domin yakar matsalar sauyin yanayi, alkawarin da suka gaza cikawa da gibin dala biliyan 16.7 a shekarar 2020.

Yanzu haka dai tasirin Sauyin Yanayi na cigaba da bayyana a sassan Afirka musamman yankin kuryar Gabashin nahiyar da kuma yammacinta, inda akalla mutane miliyan 66 suke fuskantar bala’in yunwa, saboda karancin saukar daminar da ya haifar da fari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.