Isa ga babban shafi

Guguwar Julia ta afkawa gabar tekun Nicaragua

Hukumar kula da yanayi ta Amurka ta ce guguwar Julia ta isa gabar tekun Karebiya na Nicaragua da sanyin safiyar Lahadi, mai dauke da barazanar ambaliyar ruwa da zabtarewar laka a fadin tsakiyar Amurka.

Hukumomi sun fara daukar matakan kashe mutane a yankunan da suke da hatsari
Hukumomi sun fara daukar matakan kashe mutane a yankunan da suke da hatsari REUTERS - MARCO BELLO
Talla

Hukumar kula da yanayi ta ce, an yi kiyasin iskar na da karfin gaske, inda ta yi gudun nisan mil 85 a cikin sa'a guda lokacin da ta afkawa kusa da yankin Laguna de Perlas.

Bluefields da ya kasance daya daga cikin manyan garuruwan da ke gabar tekun da ake sa ran za a yi fama da guguwar, masunta na kokarin killace kwale-kwalen su yayin da jama'a ke kokarin siyan kayan abinci da kuma cire kudi daga na'urorin ATM, domin shirin ko ta kwana.

Da tsakar dare ne aka fara jin iska mai karfin guguwa da ruwan sama kamar yadda AFP ya bayyana a birnin, yayin da kafafen yada labarai na kasar suka bayar da rahoton lalacewar rufin gidaje da faduwar bishiyoyi da kuma katsewar wutar lantarki.

Kafin isa Nicaragua, guguwar Julia ta wuce wasu tsibiran Colombia guda uku, kamar yadda wani jami'in ma'aikatar muhalli ya shaida wa AFP, lamarin da ya haddasa ruwan sama da walkiya a arewacin kasar.

Yayin da hukumomi suka bayar da rahoton cewa ba a samu asarar rayuka ko jikkata a tsibiran da ke da kusan mutane 48,000 ba, shugaban kasar Colombia Gustavo Petro ya sanya yankin a cikin yankuna mafiya hadari tare da ba da umarnin otal-otal da su bube wa masu neman mafaka.

Nicaragua ta kwashe mutane kusan 6,000 a Laguna de Perlas, dake gabar teku, da kuma wasu yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.