Isa ga babban shafi

WHO ta samar da wani shirin magance matsalolin kiwon lafiya a duniya

Hukumomin lafiya, abinci da muhalli na duniya sun fitar da wani shirin aikin hadin gwiwa na farko da nufin tunkarar duk wata annoba da ke barazana ga lafiyar mutane da dabbobi.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya kenan, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya kenan, Tedros Adhanom Ghebreyesus. © Denis Balibouse/Reuters
Talla

Shirin hadin gwiwar Kiwon Lafiya an samar da shi ne domin tunkarar duk wani kalubale da ke tunkarar halittun duniya da kuma samar da matakan kariya ko kuma rigakafi, in ji WHO.

WHO ta ce wannan wani shiri ne mai girma da ke neman inganta lafiyar mutane, dabbobi, tsirrai, da muhalli.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya uku ne suka kaddamar da shirin wato Hukumar Abinci da Aikin Noma, da Hukumar Kula da Muhalli Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma Hukumar Kula da Lafiyar Dabbobi ta Duniya.

Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, y ace ana fatan shirin na shekaru biyar wato daga 2022-2026 zai yi dukkan mai yuwuwa wajen kare duniya daga bala’o’in da ke tunkarar lafiyar dan adam, dabbobi, muhalli, musamman irin su Covid-19 da yi barna sosai ga duniya.

Kashi uku cikin hudu na duk cututtukan da ke fitowa sun samo asali ne daga dabbobi, in ji WHO yayin da take jan hankalin gwamnatoci da su kara kaimi wajen tunkarar kalubalen da ke tunkarar bangaren lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.