Isa ga babban shafi

India: An cafke mutanen da ake zargi da hannu a mutuwar mutane sama da 130

'Yan sanda a kasar India sun sanar da kama mutane 9 da ake zargin suna da hannu wajen rushewar gadar da aka samu a Jihar Gujerat wadda ta kashe mutane sama da 130.

Wasu daga cikin mutanen da ibtila'in ya rutsa da su kenan
Wasu daga cikin mutanen da ibtila'in ya rutsa da su kenan (Photo : Reuters)
Talla

Wani babban jami’in 'yan sandan yankin Ashok Kumar Yadav yace mutanen 9 da aka kama, na daga cikin ma’aikatan kamfanin dake kula da gadar a Morbi, kuma yanzu haka ana gudanar da bincike a kansu domin ganin ko za’a tuhume su da laifin aikata kisan kai.

Daruruwan baki ne suka taru akan gadar domin gudanar da bikin addini da ake kira Diwali, yayin da hotunan bidiyon da aka nada suka nuna yadda gadar ke motsawa daga bangare zuwa bangare kafin ruftawar ta.

Wani da ya tsallake rijiya da baya, Madhvi Ben yace suna tsaye akan gadar lokacin da ta katse, abinda ya kaiga mutane yin ihu da kuma neman tsira da rayukansu.

Baturen 'yan sandan yankin, P. Dekavadiya yace adadin mutanen da suka mutu a hadarin wanda ya faru a jihar Firaminista Narendra Modi ya kai 137, kuma akwai yara 50 da jariri dan wata biyu da shima ya mutu.

Wani dan majalisar yanki Kalyanji Kundariya yace iyalansa 12 ke cikin wadanda suka mutu a hadarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.