Isa ga babban shafi

Yawan al'ummar duniya na daf da kai wa biliyan 8

Majalisar dinkin Dunya ta yi kiyasin cewa yawan al’ummmar duniya zai karu zuwa biliyan 8 a tsakiyar watan Nuwamban nan da muke ciki, kuma zai ci gaba da karuwa  a hankali a cikin gwamman shekaru masu zuwa.

Yawan al'ummar duniya zai karu zuwa biliyan 8 a Nuwamba.
Yawan al'ummar duniya zai karu zuwa biliyan 8 a Nuwamba. © afp
Talla

Hukumar kula da yawan jama’a ta majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin cewa al’ummar duniya za su kai biliyan 8 a ranar 14 ga watan Nuwamba, ninki 3 kenan na yawan al’ummar duniya a shekarar 1950, lokacin da ake da mutane biliyan 2 da rabi.

Jami’ar hukumar, Rachel Snow ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa bayan karuwar da al’ummar duniya suka yi cikin sauri a cikin shekarun 1960, yanzu yana tafiyar hawainiya.

Yadda al’ummar duniya ke yaduwa ya ragu daga kashi 2 da digo 1 a tsakanin shekarun 1962 da 1965  zuwa kasa da kashi 1 a shekarar 2020.

Adadin na iya raguwa zuwa kasa da rabin kashi zuwa shekarar 2050, sakamakon yadda ake ci baya wajen samun rabo na haihuwa, kamar yadda majalisar dinkin duniyar ta yi hasashe.

Sai dai majalisar ta yi wani hasashen na dabam da ke nuni da cewa duba da yadda ake samun karin tsawon rai, inda ake kai wa shekaru 72, da kuma karuwar wadanda suka kai munzulin haihuwa, al’ummar duniya za ta ci gaba da karuwa zuwa biliyan 8 da rabi a shekarar 2030, biliyan 9 da dubu dari 7 a 2050, sannan a 2080 ya kai biliyan 10 da dubu dari 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.