Isa ga babban shafi

Dole ne kasashen duniya su daina gurbata muhalli - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci kasashen duniya da su yi duk mai yiwuwa don rage dumamar yanayi ta hanyar rage yawan hayaki da tururin da masana’antunsu ke fitarwa. Shugaban ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga mahalarta taron yaki da matsalar dumamar yanayi da ke gudana yanzu haka a Sharm El-Sheikh da ke Masar.

Shugaban Amurka Joe Biden a wurin taron sauyin yanayi a Masar.
Shugaban Amurka Joe Biden a wurin taron sauyin yanayi a Masar. REUTERS - MOHAMED ABD EL GHANY
Talla

A Jawabin nasa, Joe Biden ya ce Amurka na iya kokarinta don sauke nauyin da ya rataya a wuyenta wajen rage sinadiran da ke taimaka wa gurbata muhalli, saboda haka akwai wajabcin sauran kasashe su yi koyi da ita don cimma nasara.

A cikin jawabin nasa na mintuna 22, shugaban na Amurka ya ce ‘matukar muna son yin nasara a wannan gwagwarmaya, akwai bukatar kowace daga cikin manyan kasashe ta tabbatar da cewa tana mutunta yarjeniyoyin da aka kulla a baya dangane da wannan batu’’.

Karkashin yarjejeniyar da aka amince da ita a taron dumamar yanayi da ya gudana a 2015 a birnin Paris, illahirin kasashen duniya ciki har da wadanda ke da manyan masana’antu, sun amince, sannnu a hankali za su sauya hanyoyin da suka saba amfani da su wajen samar da makamashi, yayin da za su zuba makudan kudade wajen tunkarar matsalar.

Joe Biden ya yada zango a birnin Sharm el-Sheikh ne a hanyarsa ta zuwa Cambodia don halartar taron kasashen kudancin Kudu maso gabashin Asiya, da kuma taron G20 da ya zai hada kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya da za a yi cikin makon gobe a Indonesia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.