Isa ga babban shafi

Sabon makamin da Korea ta Arewa ta harba zai iya kaiwa Amurka- Japan

Korea ta Arewa ta sake gudanar da sabon gwajin makami mai linzami nau’in ICBM da ke tsallake nahiya zuwa nahiya a yau juma’a inda ya sauka a gab da tekun Japan irinsa na biyu mafi girma da kasar ta harba cikin watan nan, wanda kuma ake ganin zai iya kaiwa wani yanki na Amurka.

Hoton Gwajin makamin da Korea ta Arewa ta yi a yau juma'a.
Hoton Gwajin makamin da Korea ta Arewa ta yi a yau juma'a. REUTERS - HEO RAN
Talla

Ministan tsaron Japan Yasukazu Hamada ya shaidawa taron manema labarai cewa nau’in makamin na Korea ta Arewa zai iya mamaye ilahirin tsandaurin Amurka.

Kididdigar da Korea ta kudu da Japan suka gudanar ta ce makamin ya yi gudun kilomita dubu dubu 6 zuwa dubu 6 da 100 a sararin samaniya fiye da yadda nau’insa na ICBM ya saba yi sararin samaniya.

Manyan hafsoshin Sojin Korea ta Kudu sun ce Korea ta Arewan ta harba makamin na ICBM da misalin karfe 10:15 inda makamin ya nufi arewacin gabar ruwan kasar  gabanin sauka a yammacin Hokkaido, makamin da Japan ta ce gudunsa da kuma girmansa ya zarta wanda kasar ta saba gwadawa a baya.

Tuni Amurka ta yi kakkausar suka ga sabon gwajin na Korea ta Arewa tare da shan alwashin daukar matakin kare jama’arta da kuma abokananta da ke Asiya dai dai lokacin da mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ke shirin ganawa da shugabannin kasashen Japan da Korea ta Kudu da Australia da New Zealand da kuma Canada a Bangkok don tattaunawa kan gwajin makamin da Korea ta Arewa ta yi a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.