Isa ga babban shafi

UNESCO ta bayyana damuwa kan yadda dumamar yanayi ke barazana ga wuraren tarihi

Yayinda ake kawo karshen taron magance matsalar sauyin yanayin da aka yi wa lakabi da COP27 a kasar Masar, Hukumar UNESCO ta bayyana damuwa akan yadda matsalar sauyin yanayin ke illa ga wasu wuraren tarihin da ke fadin duniya.

Guda cikin wuraren tarihin da Ambaliyar ruwa ta yiwa illa a Pakistan.
Guda cikin wuraren tarihin da Ambaliyar ruwa ta yiwa illa a Pakistan. AP - Sergei Grits
Talla

Hukumar UNESCO ta ce ambaliyar ruwan da aka samu wadda ta haifar da matsala a birane da kauyuka wadanda ke cikin illolin sauyin yanayi na barazana ga yankuna da dama da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana su a matsayin wuraren tarihi saboda dalilan da ke da nasaba da haka.

Hukumar ta ce a kasar Pakistan da ta gamu da ambaliyar da bata taba gani ba, iftila’in ya yi matukar illa a yankin Sindhm abinda ya kai ga mutuwar mutane sama da 1,600 tare da jikkata wasu da dama, baya ga asarar dukiyoyi da gidaje.

Daraktan adana kayan tarihi na hukumar Lazare Elundu Asare ya kuma bayyana cewar ambaliyar ta yi barazanar kawar da wani sashe na wurin tarihin Mahenjo Daro, amma daga bisani ya sha da kyar.

Jami’in ya ce wannan alamu ne da ke nuna girmar matsalar da kuma irin illar da take haifarwa a doron kasa ba tare da la’akari da yanki ko kasa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.