Isa ga babban shafi

Duniya baki daya ta tsunduma cikin rashin ruwa - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, daukacin yankunan duniya sun gamu da ibtila’in ambaliyar ruwa da kuma pari a shekarar da ta gabata, yayin da biliyoyin mutane suka rasa wadataccen ruwa mai tsafta.

Wasu kananan yara a gabar ruwa, suna shan ruwan famfo
Wasu kananan yara a gabar ruwa, suna shan ruwan famfo Getty Images/Gallo Images/Danita Delimont
Talla

Hukumar Kula da Yanayi ta Majalisar Dinkin Dunitya ta ce, yankuna da dama na doran-kasan da muke rayuwa a kai, sun kafe fiye da yadda aka saba gani a shekarar 2021.

Rahoton hukumar ya yi nazari kan yadda sauyain yanayi ya yi tasirin  kan samun ruwa , yayin da kimanin mutane biliyan 3 da miliyan 600 ke  fuskantar karancin ruwan na tsawon akalla wata guda a shekara.

Rahoton ya ce,  akwai yiwuwar adadin masu fuskantar karancin ruwan ya karu zuwa fiye da biliyan biyar nan da shekara ta 2050.

A ewar rahoton, kasha 74 cikin 100 na ibtila’o’in da aka gani a duniya a shekara ta 2001 da 2018 , na da nasaba da ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.