Isa ga babban shafi

An tsare 'yan jaridu 533 tare da kashe 57 a bakin aikinsu a 2022 - RSF

Adadin ‘yan jaridar da ake tsare da su a duniya ya kai 533 a wannan shekarar ta 2022 wanda shine kololuwar adadin ta aka taba gani a duniya, sabanin 488 da aka gani a bara, yayin da aka kashe ‘yan jaridu 57.

Wasu 'yan jaridu yayin gudanar da aikinsu
Wasu 'yan jaridu yayin gudanar da aikinsu AP - Tony Avelar
Talla

Hakan na kunshe ne cikin rahotan da kungiyar kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya Reporters Without Borders (RSF) ta fitar wannan Laraba 14 ga watan Disambar 2022.

Rahotan RSF yace mummunan matakin murkushe zanga-zangar da mahukuntan Iran ke yi, ya taimaka wajen kara adadin 'yan jaridun da ake tsare a duniya.

A cewar kungiyar RSF mai cibiya a Faransa, adadin ya tashi ne daga 488 da ake da shi a shekarar 2021, adadi mafi muni da aka taba gani tun a baran.

Kasashe biyar

Rahoton yace fiye da rabi na wannan adadin ‘yan jaridu 533 ana tsare da su a kasashe biyar kachal: har yanzu China ta kasance kasar da ke tsare da adadi mafi yawa da ‘yan jaridu a duniya, inda ta garkame 110,  Myanmar na da 62 sai Iran da 47, Vietnam na da 39 sai kuma Belarus da ta kama ‘yan jaridu 31.

Shugaban kungiyar ta Reporteur Sans Frontier Christophe Deloire, yace Gwamnatotin kama-karya da na mulkinn danniya na cika gidajen yarinsu cikin sauri fiye da kowane lokaci ta hanyar kame 'yan jaridu.

Iran

Iran ce kasa daya tilo da ba ta cikin jerin kasashe da suke tsare da ‘yan jaridu a bara, acewae RSF, da ta fara bin diggigin ‘yan jaridu dake bacewa tun a shekarar 1995.

Yawan ‘yan jaridu mata da ke gidan yari kuma ya kai wani matsayi a duniya, wanda ya karu daga 60 zuwa 78 tun daga shekarar 2021, saboda yadda mata suka fara shiga wannan aiki na sadaukarwa.

Yawan adadin 'yan jaridun da aka kashe ma ya karu -- zuwa 57 – daga 48 da 50 a shekaru biyu da suka gabata saboda yakin da ake yi a Ukraine.

RSF ta ce kusan kashi 80 cikin 100 na kwararrun harkar yada labarai da aka kashe a duniya a shekarar 2022, na da alaka da ayyukansu ko labaran da suke yadawa”, kamar  bincike kan aikata laifuka ko cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.