Twitter ya dakatar da shafukan 'yan jaridu da ke sukar Elon Musk
Kamfanin sadarwar zamani mai dandalin sada zumunta na Twitter ya dakatar da shafukan wasu ‘yan jarida da suka yi ta rubutu na caccaka a game da shi da sabon mamallakinsa Elon Musk.
Wallafawa ranar:
Talla
Wasu daga cikin ‘yan jaridar da wanna lamari ya shafa suna rubutu ne a kan rufe shafukan wasu mutane tare da bibiyarsu a asirce.
Mista Musk ya dauki salon tilasta wa ‘yan jarida yin shuru, a yaayin da yake ikirarin fafutukar ‘yancin fadin albarkacin baki, lamarin da ya janyo cece kuce a baya bayan nan, ya kuma haddasa rabuwarsa da dimbin masu talla.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu