Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci baiwa kananan kasashe Dala biliyan 20 saboda sauyin yanayi

Wani daftarin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya na ceto yanayi ya yi kira ga kasashe masu arziki da su kara taimakon kudi ga kasashe masu tasowa zuwa dala biliyan 20 daga nan zuwa shekarar 2025, da kuma karin da zai kai dala biliyan 30 a kowace shekara nan da shekarar 2030.

Wasu 'yan Afganistan kenan da ke tafiya a gefen wata hanya da baraguzai ya toshe sakamakon zaftarewar laka, a lardin Parwan da ke arewacin Kabul a Afghanistan, Alhamis, 27 ga Agusta, 2020. Yawan mutanen da suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a arewaci da gabashin Afghanistan a wancan lokacin sun karu zuwa akalla 150, da dama sun jikkata yayin da ma’aikatan ceto ke neman wadanda suka tsira a karkashin laka da baraguzan gidajen da suka ruguje.
Wasu 'yan Afganistan kenan da ke tafiya a gefen wata hanya da baraguzai ya toshe sakamakon zaftarewar laka, a lardin Parwan da ke arewacin Kabul a Afghanistan, Alhamis, 27 ga Agusta, 2020. Yawan mutanen da suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a arewaci da gabashin Afghanistan a wancan lokacin sun karu zuwa akalla 150, da dama sun jikkata yayin da ma’aikatan ceto ke neman wadanda suka tsira a karkashin laka da baraguzan gidajen da suka ruguje. AP - Rahmat Gul
Talla

Har ila yau, MDD ta yi kira ga kasashe da su tabbatar da cewa nan da shekara ta 2030 a kalla kashi 30 cikin 100 na yankunan kasa, da ruwa, da gabar teku da tsibirai sun samu kariya daga lalacewa.

Daftarin, wanda kasar China ta jagoranci fitar da shi, bayan taron koli mai suna COP15 a Montreal da ta shirya, ya samu karbuwa cikin gaggawa daga masu rajin kare muhalli, ko da yake har yanzu akwai bukatar goyon bayan kasashe 196 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kare halittu kafin a kammala shi.

Bayanin daftarin ya nuna cewa kasar China a shirye take ta jagoranci shirin bisa burin da kasashe suka nuna a lokacin COP15," in ji Alfred DeGemmis, na kungiyar rajin kare namun daji.

DeGemmis ya kuma yi gargadin duk da haka cewa yawancin abubuwan da ke cikin daftarin sun fi mayar da hankali kan yadda za yaki dumamar yanayin nan da shekarar 2050, sabanin nan da 2030.

Kasashe masu karamin karfi sun yi nuni da cewa kasashen da suka ci gaba sun samu arziki ta hanyar amfani da albarkatunsu don haka ya kamata a biya su don kare muhallin su.

Adadin kudaden shiga da kasashe masu tasowa ke samu a yanzu an kiyasta kusan dala biliyan 10 a kowace shekara.

Wakilai na musamman na aiki don magance barnar da gurbacewar yanayi ya haifar ga nau'in tsirrai da dabbobi kimanin miliyan guda ciki kuwa har da bacewar wasu halittu daga doron kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.