Isa ga babban shafi

Kotu a Birtaniya ta amince da matakin tasa keyar bakin haure zuwa Rwanda

Kotu a birnin Landan ta tabbatar da halascin shirin gwamnatin Birtaniya na tasa keyar bakin haure zuwa kasar Ruwanda, bayan kalubalantar matakin da bakin haure da masu fafutuka suka yi.

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak kenan
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak kenan AP - Henry Nicholls
Talla

Tsohon firaministan Boris Johnson ne ya kawo shawarar yin kokarin magance yawan bakin hauren da ke tsallakawa tsibirin Channel daga arewacin Faransa da kananan jiragen ruwa.

Amma shirin ya haifar da zanga-zanga daga kungiyoyin kare hakkin jama'a da kuma kungiyoyin agaji, inda matakin shari'a na karshe da aka dauka ya yi nasarar dakile tashin jirgin na farko a watan Yuni.

Kungiyoyi masu tallafawa bakin haure sun gabatar da kara a babbar kotun birnin Landan domin gudanar da shari'a a kan manufar, suna masu ikirarin cewa ba ta bisa ka'ida.

Lauyoyin sun yi zargin cewa manufar ta sabawa doka bisa dalilai da dama, ciki har da yadda aka tantance Rwanda a matsayin kasa ta uku.

Alkalan dai sun amince cewa batun ya tada muhawara a tsakanin jama’a amma sun ce abin da ya rage shi ne a tabbatar da an fahimci doka da kyau da kuma kiyaye hakokin da majalisar ta ba su.

Sai dai alkalan sun ce ministar harkokin cikin gida Suella Braverman ba ta yi la'akari da yadda was uke kalubalantar shari'ar ba, inda suka mayar da shari'ar nasu zuwa gare ta.

Fiye da bakin haure 43,000 ne suka tsallaka tsibirin Channel a bana.

Magajiyar Boris Johnson wato Liz Truss da kuma wanda ya gaje ta Rishi Sunak sun goyi bayan yarjejeniyar Rwanda, da ke da nufin tura duk wanda ake ganin ya shiga Birtaniya ba bisa ka'ida ba tun ranar 1 ga Janairu zuwa kasar da ke yankin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.