Isa ga babban shafi

Rasha ta hana sayar da makamashi don kuntatawa kasashen Turai

Kasar Rasha ta fitar da wata doka ta haramta sayar da mai ga kasashe da kamfanonin da suka mutunta farashin mai da kasashen yammacin duniya suka amince da shi kan harin da Moscow ta kai Ukraine.

Shugaban Rasha Vladmir Putin.
Shugaban Rasha Vladmir Putin. Alexey Filippov/RIA Novosti
Talla

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, an haramta samar da mai da dangoginsu na Rasha ga kasashen waje da wasu daidaikun mutane.

Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga Fabrairu har zuwa 1 ga Yulin 2023.

Sanarwar ta kara da cewa ana iya dage haramcin a cikin sharuddan da shugaba Vladimir Putin ya gindaya.

Farashi na dala 60 kan kowacce ganga da Tarayyar Turai da G7 da Australia suka amince da shi ya fara aiki ne a farkon watan Disamba tare da neman dakilewa Rasha samun kudaden shiga domin tabbatar da cewa Moscow ta samu nakasu a kasuwannin duniya.

Takunkumin da Tarayyar Turai ta sanya a kan isar da danyen mai na Rasha a teku, da nufin tabbatar da cewa kasar ba za ta iya tsallake takunkumin ba, ta hanyar sayar da mai ga kasashe uku a farashi mai tsada na gab da fara aiki.

Rasha dai ta ce matakin ba zai shafi yakin da ta ke yi na soji a Ukraine ba, ta kuma bayyana kwarin gwiwarta na samun sabbin masu sayen makamashi daga gareta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.