Isa ga babban shafi

'Yan gudun hijirar Rohingya 200 sun isa Indonesia bayan shafe wata guda a saman teku

Ma’aikatan agaji sun karbi 'yan gudun hijirar Rohingya yayin da wani jirgin ruwa dauke da mutane kusan 200 ya isa gabar teku a Indonesia bayan shafe tsawon wata guda yana tafiya a kan ruwa, inda hukumomi suka ce, a karo na hudu kenan da aka karbi ire-iren wadannan bakin a gabar teku a ‘yan watannin nan.

Irin kwale kwalen da bakin haure ke yawan amfani da shi wajen ketare Meditareniya.
Irin kwale kwalen da bakin haure ke yawan amfani da shi wajen ketare Meditareniya. Photo transmise à RFI par un migrant
Talla

A kowace shekara dubban ‘yan kabilar Rohingya akasari musulmi, wadanda ke fuskantar cin zarafi sosai a kasar Myanmar mai mabiya addinin Buddha, suna kasadar yin doguwar tafiya ta ruwa, galibi a cikin jiragen ruwa marasa inganci duk dai a kokarinsu na isa Malaysia ko Indonesia.

Jirgin ruwan katako ya isa yankin ne da misalin karfe 5:30 na yamma (10:30 agogon GMT) a gabar teku a lardin Aceh da ke yammacin Indonesia, in ji kakakin 'yan sandan yankin Winardy.

'Yan gudun hijirar Rohingya dari da tamanin da biyar sun sauka a Pidie, adadin ya kunshi maza 83, mata 70 da kuma yara 32.

Sanarwar da hukumomi suka fitar ta ce, ‘yan gudun hijira na karbar kulawa daga likitoci, inda marasa lafiya ke karbar agaji na wucin gadi.

Ba a samu cikakken bayani kan yanayin tafiyar tasu ba, sai dai wani matashi daga cikin su ya ce sun taso ne daga kasar Bangladesh.

Jirgin ruwan na ranar Litinin a Aceh ya zo ne kwana guda bayan wani jirgin ruwa dauke da 'yan gudun hijirar Rohingya 57 ya isa bakin teku a lardin bayan tafiyar tsawon guda a cikin teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.