Isa ga babban shafi

Mabiya darikar Katolika sun fara bankwana da gawar Fafaroma Benedict

Dubban mabiya darikar katolika ne suka kai gaisuwar ban girma ga tsohon Fafaroma Benedict na 16 a fadar Vatican ranar litinin, yayin da gawarsa ke kwance a cocin St Peter's Basilica kafin jana'izar sa.

Yadda aka ajiye gawar Fafaroma Benedict na 16 kenan a St. Peter's Basilica
Yadda aka ajiye gawar Fafaroma Benedict na 16 kenan a St. Peter's Basilica © KAI PFAFFENBACH / REUTERS
Talla

Kiristoci da dama ne suka jerin gwano tun kafin wayewar gari domin yin bankwana da gawar Bajamushen, wadda aka dauke ta da sanyin safiyar Litinin daga fadar Vatican wato inda ya rasu kenan ranar Asabar din da ta wuce yana da shekara 95.

Benedict ya jagoranci Cocin Katolika na tsawon shekaru takwas kafin ya zama Fafaroma na farko a cikin karni shida da ya sauka daga mulki a shekara ta 2013, bisa la'akari da matsala ta lafiya da ya samu.

Magajinsa Fafaroma Francis ne zai jagoranci jana'izar ranar Alhamis a dandalin St Peter kafin a ajiye gawarsa a cikin kaburburan da ke karkashin ginin basilica.

Gawar Benedict, sanye da jajayen rigunan na Fafaroma da kuma riga mai ratsin zinare, an ajiye ta a cikin wani akwatin gawa da aka lullube da farin kyalle.

Gawarsa za ta kwanta a wannan wuri tsawon kwanaki uku, domin bawa mabiya addinin kirista damar yin bankwana da gawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.