Isa ga babban shafi

Alexei Navalny na fama da alamu masu kama da mura a gidan yari

Dan adawar Rasha Alexei Navalny, wanda aka daure shekaru biyu a gidan yari, ya fada a yau Laraba cewa yana fama da alamu masu kama da mura kuma an hana shi samun gamsasshen kulawa, magoya bayansa sun yi tir da yunkurin da fadar Kremlin ta yi na "kashe shi a hankali.

 Alexei Navalny Dan adawa ga shugaban kasar Rasha
Alexei Navalny Dan adawa ga shugaban kasar Rasha AP - Denis Kaminev
Talla

Daga inda ake tsare da shi ,Alexeï Navalny zai halarci kararraki uku a rana ta hanyar bidiyo game da koke-koke game da takunkumin da hukumar gidan yari ta yi masa.

Alexeï Navalny ya yi magana a gaban alkali inda ya nemi a dage sauraren wadannan kararraki uku saboda dalilai na kiwon lafiya.

Alexei Navalny, mai shekaru 46, ya ce dole ne ya yi gwagwarmayar don samun "magungunan yau da kullun" kuma an hana shi zuwa asibiti a sashin kula da lafiya na gidan yarin da ke da nisan kilomita 200 daga Moscow.

Alexeï Navalny ya na mai cewa ya dauki kwanaki hudu don samun ruwan zafi kadan," in ji shi, labarin da masu wakiltar sa suka ruwaito, yana mai ikirarin cewa ya na fama da "zazzabi da tashin hankali".

A shafin Instagram, matarsa, Yulia Navalnaïa, ta zargi hukumomin gidan yarin da ƙin kula da mijinta da kuma “ɓatanci” yanayin tsare shi. Ta tambaye su.

Kusan likitocin Rasha 500 ne suka rattaba hannu kan wata takardar koke da aka wallafa a shafin Facebook, inda suka yi kira ga Vladimir Putin da ya bai wa  Navalny kulawar da ta dace da kuma kawo karshen cin zarafi da ake yi masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.