Isa ga babban shafi

Ana zaton kowa ya mutu a hadarin jirgin Nepal

Hukumomin Nepal sun debe tsammanin gano mutun ko guda da ke da sauran numfashi a hatsarin jirgin sama da ya auku a jiya Lahadi a kasar.

Ramin da jirgin ya fada a cikinsa kafin ya kama da wuta.
Ramin da jirgin ya fada a cikinsa kafin ya kama da wuta. © via REUTERS / HANDOUT
Talla

Jirgin ya yi hatsari ne dauka da mutane 72, inda ya fadi a wani kwari kuma nan take ya kama da wuta.

Har yanzu babu cikakken bayani kan musabbabin aukuwar hatsarin, amma wani hoton bidiyo da aka watsa a shafukan sada zumunta, wanda kuma Kamfanin Dillancin Labarai na AFP da abokin hadin guiwarsa, ESN suka tabbatar da sahihancinsa, ya nuna yadda jirgin ke karkatowa zuwa bangaren hago a daidai lokacin da yake shirin fadowa.

Sojojin kasar sun yi amfani da igiyoyi wajen kwaso gawarwaki daga cikin ramin da jirgin ya fada a ciki mai nisan mita 300.

A yau Litinin, al'ummar kasar na zaman makoki domin nuna alhinin mutuwar fasinjojin wannan jirgin, amma sojojin sun dakatar da aikin neman sauran gawarwakin har sai zuwa gobe.

Yanzu haka gawarwakin mutane 68 na hannun hukumomin kasar, inda ake ci gaba da neman sauran gawarwaki uku.

Hatsarin dai shi ne mafi muni da Nepal ta gani cikin shekaru 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.