Isa ga babban shafi

Oxfam ta bukaci a karya arzikin attajiran duniya

Kungiyar Agaji ta Oxfam ta bukaci mahukunta da su rage adadin masu arziki na duniya nan da shekara ta 2030, ta hanyar lafta musu  haraji domin samara da daidaito tsakaninsu da matalauta.

An bude taron tattalin arziki a Davos
An bude taron tattalin arziki a Davos AP - Markus Schreiber
Talla

Oxfam ta yi wannan kiran ne a daidai lokacin da aka bude taron tattalin arziki na duniya a Davos na kasar Switzerland da ke samun halartar shugabannin siyasa da manyan attajirai da fitattun mutane.

 A wani rahoto da ta fitar gabanin bude taron, Oxfam ta ce, mawadata masu biliyoyin kudi, sun rubanya arzikinsu a cikin shekaru 10 da suka gabata.

A cewarta, attajiran duniya sun kara samun makuden kudade a daidai lokacin da rayuwa ta yi wa talakawa tsada saboda bullar cutar Covid-19, ga kuma tashin farashin abinci da makamashi saboda yakin Rasha da Ukaine.

Daga shekara ta 2020, arzikin attajiran ya karu da  Dala biliyan 2 da miliyan 700 a rana guda, duk da cewa tsadar rayuwa ta hana ma’aikata biliyan 1 da dubu 700 morar albashinsu yadda ya kamata.

Yanzu haka Oxfam na kira da a lafta wa attajiran karin kudaden haraji domin rage ratar da ke tsakaninsu da  talakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.