Isa ga babban shafi

Za mu samu galaba kan Ukraine - Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce babu tantama kasarsa za ta samu nasara a yakin da take ci gaba da gwabzawa da Ukraine duk da wasu ‘yan koma-bayan da suka samu a ‘yan watannin baya. 

Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da  sojojinsa.
Shugaban Rasha Vladimir Putin tare da sojojinsa. AP - Mikhail Klimentyev
Talla

Yayin da yake jawabi ga taron ma’aikata a birnin Saint Petersburg, Putin ya ce duk da wasu nasarorin da aka samu a kan sojojinsu, yana da yakinin cewar za su samu galabar yakin. 

Shugaban ya ce hadin kai da goyan bayan mutanen Rasha da kuma jajircewar gwarazan sojojin kasar tare da ayyukan da kamfanonin sojin kasar ke yi wajen sarrafa makamai zai taimaka musu wajen samun nasarar da suke bukata. 

Putin ya kuma yaba wa kamfanin sarrafa makamai masu linzamin kasar na Almaz-Antey wanda ya ce yana taka rawa ta musamman wajen samar musu da kayan da suke bukata domin ci gaba da tunkarar yakin. 

Shugaban na Rasha na ziyarar mahaifarsa da ke Saint Petersburg ne domin bikin cika shekaru 80 na samun nasarar da sojojin Rasha suka yi wajen murkushe boren da aka yi a birnin Leningrad. 

Kalaman shugaban na zuwa ne wata guda bayan ya sauya kwamandan sojinsa da ke jagorancin yakin Ukraine, abin da ya haifar da tasgaro a yakin da kasarsa ke yi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.