Isa ga babban shafi

Jami'an gwamnatin Ukraine da dama sun yi murabus

Jami'an gwamnatin Ukraine da dama sun yi murabus a ranar Talatar nan, bayan da Ma'aikatar Tsaron Kasar ta shiga rudani sakamakon zarge-zargen badakalar sayen kayan abinci, wadda ta haifar da zargin cin hanci da rashawa mafi girma da kasar ta fuskanta tun farkon mamayar da Rasha ta yi mata. 

Wasu daga cikin manyan jami'an tsaron Ukraine
Wasu daga cikin manyan jami'an tsaron Ukraine via REUTERS - LEHTIKUVA
Talla

Wannan badakalar ta shafi mataimakin Ministan Tsaron Kasar ta Ukraine Vyacheslav Shapovalov da mataimakin babban jami’in gudanarwa a fadar shugaban kasar Kyrylo Tymoshenko da kuma mataimakin mai gabatar da kara na kasar Oleksiy Symonenko. 

Ma'aikatar Tsaron kasar ta sanar da murabus din Shapovalov, wanda ke kula da tallafin kayan aiki na rundunar, bisa zargin sa da hannu kan tashin farashin kayan abinci. 

Sai dai a cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta ce zarge-zargen ba su da tushe.

Kasar Ukraine na da tarihin cin hanci da rashawa, sai dai kuma duk kokarin da ake na kawar da lamarin a kasar abin ya ci tura. 

A shekarar 2021, kungiyar yaki da cin hanci da rasha ta Transparency International ta ce, Ukraine na matsayi na 122 daga cikin jarin kasashe 180 da ke fama da cin hanci da rashawa a duniya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.