Isa ga babban shafi

Shugaban kungiyar Wagner ya yi ikirarin kwace wani yanki kusa da Bakhmout

Shugaban kungiyar sojin haya ta Rasha Wagner ya sanar a yau Lahadi  cewa dakarunsa sun kwace garin Krasna Hora na kasar Ukraine da ke da tazarar kilomita kadan daga arewacin Bakhmout, wanda Moscow ke kokarin kwacewa tsawon watanni da dama.

Yankin Bakhmout
Yankin Bakhmout AP - Libkos
Talla

Yevgeny Prigojine, wanda ma'aikatar yada labaransa ta ruwaito cewa labarin kwace garin Krasna Hora.

Dakarun Rasha sun kara karfafa matsugunan su a arewacin Bakhmout, tare da katse wata muhimmiyar hanyar samar da kayayyaki ta Ukraine, da kuma Vougledar, inda suke kai farmaki, in ji wani jami'in mamaya na Rasha a ranar Juma'a da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Rasha ya ruwaito cewa Denis Pushilin, wani jami'in 'yan awaren a kusa da Bakhmout, cibiyar fada a gabashin Ukraine, sojojin Rasha sun "kara karfafa matsayinsu a yankin arewacin kasar.

Rasha ta kai wani “babban hari” a ranar Juma’a tare da makamai masu linzami da bama-bamai a kai kan wasu wuraren makamashi a Ukraine, bayan Volodymyr Zelensky ya zagaya Turai don neman karin makamai.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.