Isa ga babban shafi

Najeriya ta bayar da dala miliyan 1 ga wadanda girgizar kasa ta shafa a Turkiya

Tawagar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari karkashin Jagorancin ministan birnin Tarayya Abuja Mallam Muhammad Bello ta mika tallafin tallafin dala miliyan 1 ga gwamnatin Turkiya don tallafawa mutanen da ibtila’in girgizar ya shafa a kasar.

Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa na Turkiya Recep Tayyib Erdogan.
Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari da takwaransa na Turkiya Recep Tayyib Erdogan. © Presidency of Nigeria
Talla

Tawagar wadda ta samu tarba ta musamman daga jakadan Turkiyyan Mevlut Cavusoglu a ma’aikatar wajen kasar da ke birnin Ankara, jakadan yay aba da kokarin Najeriya wajen bayar da wannan tallafi.

Tawagar jami’an gwamnatin Najeriyar ta kuma ziyarci yankunan da ibtila’in girgizar kasar ya yiwa barna tare da kashe mutane kusan dubu 50 ciki har da dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar Ghana Christian Atsu.

A ranar 6 ga watan Fabarairun da muke ne girgizar kasa mai karfin maki 7.8 ta afkawa sassan Turkiya da Syria wadda aka bayyana da mafi muni da kasar ta gani a tarihi.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dai bai samu sukunin iya kai ziyarar jaje kasar ta Turkiyya ba saboda shirye-shiryen da kasar ke yin a zaben shugaban kasa a wancan lokaci.

Sai dai tawagar ta mika wasika ta musamman da Buharin ya aikewa gwamnatin Turkiyya don jajanta mata game da ibtila’in.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.