Isa ga babban shafi

Kumbon SpaceX ya isa duniyar saman jannati

‘Yan saman Jannati hudu sun isa tashar binciken sararin samaniya a yau Jumu’a bayan kumbon da ke dauke da su na SpaceX Dragon ya isa tashar cikin nasara kamar yadda wani hoton bidiyon  Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA ya nuna.

Lokacin da jirgin SpaceX ya tashi
Lokacin da jirgin SpaceX ya tashi © AP / Chris O'Meara
Talla

Kumbon na SpaceX Dragon ya isa tashar binciken sararin samaniyar ne da misalin karfe 6 da minti 40 agogon GMT a yau Juma’a kamar yadda NASA ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.

‘Yan saman Jannatin hudu sun hada da Stephen Bowen da Warren Hoburg, dukkaninsu ma’aikatan NASA, sai kuma Andrey Fedyaev na Rasha da Sultan Al-Neyadi na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sun dai isa tashar binciken sararin samaniyar ne bayan sun shafe tsawon sa’o’i biyu suna tafiya a cikin kumbon na SpaceX Dragon.

‘Yan Saman Jannatin za su shafe tsawon watanni shida a can tashar sararin samaniyar, inda za su gudanar da binciken kimiya da fasaha daban-daban har sama da 200.

Har yanzu binciken sararin samaniya na ci gaba da zama wani bangare da ke hada alakar Amurka da Rasha tun bayan da Moscow ta kaddamar da yaki kan Ukraine, lamarin da ya haddasa gaba tsakanin manyan kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.